Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
HKSAR ta yi Allah wadai da masu zanga-zanga da su kai hari kan ofishin wakilin gwamnatin tsakiyar kasar Sin
2019-07-22 14:09:04        cri

Hukumar gudanarwar yankin musamman na Hong Kong (HKSAR), ta yi Allah wadai da matakin da masu zanga zanga suka dauka na kaddamar da hari kan ofishin wakilin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin dake HKSAR.

Kakakin hukumar HKSAR ya ce, ofishin wakilin yana daya daga cikin ofisoshin da gwamnatin tsakiya ta kafa a HKSAR kuma yana gudanar da muhimman ayyuka da suka dace da tsarin mulkin kasa.

Kakakin ya ce, hukumar ta HKSAR ta yi Allah wadai da babbar murya ga masu zanga-zangar wadanda suke zazzafar adawa da kalubalantar matsayin ikon gwamnatin tsakiya ta hanyar kaddamar da hari kan ginin ofishin wakilin da kuma yunkurin lalata alamar tambarin kasa dake wajen.

Hukumar gudanarwar ta ce, ta nuna damuwarta bisa yadda wasu tsirarun 'yan adawa ke kokarin haddasa gangamin masu zanga-zanga bisa wani cikakken shirin da suka tsara, suna kalubalantar dokokin kasa, har ma sun kai hari kan ofishin wakilin gwamnatin tsakiya dake yankin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China