Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Barkewar annobar cutar Ebola a Kongo ta zama babbar barazana a gabashin Afrika
2019-06-13 11:12:52        cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce barkewar annobar cutar Ebola a jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC) ta kasance a matsayin babbar barazanar lafiya ga zamantakewar al'ummar shiyyar gabashin Afrika.

Tigest Ketsela Mengestu, wakiliyar hukumar ta WHO a kasar Tanzania, ta bukaci kungiyar kasashen gabashin Afrika (EAC) ta cigaba da gudanar da tsare tsaren da zasu taimakawa kasashen da ma shiyyar baki daya wajen tabbatar da daukar matakan rigakafin cutar, da kai daukin gaggawa da kuma takaita barazanar lafiya da cutar ke iya haifarwa.

Ta ce annobar cutar Ebola data barke a DRC kawo yanzu ta shafi mutane sama da 1,900 kana tayi sanadiyyar mutuwar mutane 1,300.

Jami'ar ta bayyana hakan ne a Namanga dake kan iyakar kasashen Tanzania-Kenya, a lokacin da ta kai wata ziyarar aiki domin kaddamar da wani babban shirin dakile cutar akan iyakokin kasashen biyu, inda ake fargabar yiwuwar barkewar cutar.

Mengestu ta kara da cewa, shirin zai taimakawa kasashen EAC wajen gano irin raunin da ake dashi da kuma bangarorin da ake bukatar a kara bunkasawa wajen daukar matakan da suka dace.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China