![]() |
|
2019-06-18 11:07:21 cri |
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana farin cikinsa sakamakon yadda ake samun raguwar yaduwar cutar Ebola a manyan yankuna biyu da cutar ta fi kamari a jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC).
A wata sanarwar hadin gwiwa ta hukumar WHO, da ma'aikatar lafiyar kasar Uganda suka fitar a ranar Litinin, Tedros ya ce, yanayin da ake ciki game da cutar Ebola a DRC ya kasance mai sarkakiya yana kwan-gaba-kwan-baya.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China