Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon haraji zai dakile nasarar tattaunawa tsakanin Sin da Amurka
2019-07-17 20:30:07        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce har kullum burin Sin shi ne warware sabanin tattalin arziki da cinikayya tsakanin ta da Amurka ta hanyar tattaunawa.

Geng Shuang ya bayyana hakan ne a yau Laraba, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, yana mai cewa Sin na shiga dukkanin tattaunawa da kyakkyawar zuciya.

Ya ce idan har Amurka ta sanya sabon haraji kan hajojin da Sin ke shigarwa yankunan ta, to ko shakka babu hakan zai haifar da tarnaki ga shawarwarin da sassan biyu ke yi, kana hakan zai tsawaita lokacin cimma yarjejeniya.

Daga nan sai jami'in ya yi kira ga Amurka, da ta nuna kyawun manufa, ta kuma yi hadin gwiwa da Sin, wajen daukar matakan da za su kai ga cimma yarjejeniyar da za ta amfani sassan biyu, ta hanyar martaba juna da kuma yanayi na daidaito.

A jiya Talata ne dai shugaban Amurka Donald Trump, ya shelanta cewa, akwai sauran rina a kaba, game da batun takaddamar dake tsakanin kasar sa da Sin, yana mai barazanar kara sanyawa hajojin kasar ta Sin da darajar su ta kai dala biliyan 325 sabon haraji.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China