Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kalaman Amurka ba su da tushe
2019-07-16 20:39:52        cri

Yayin taron ganawa da manema labarai na yau Talata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, kalaman da Amurka ta fada cewar wai kasar Sin, tana fatan za ta daddale yarjejeniya tsakaninta da Amurka cikin gaggawa, saboda kaucewa tafiyar hawainiyar ci gaban tattalin arzikinta batu ne maras tushe ko makama.

A jiya Litinin ne shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya bayyana ta shafin sa na Twitter cewa, saurin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a cikin rubu'i biyu shi ne mafi karanta, a cikin shekaru 27 da suka gabata, kuma kamfanoni sama da dubu goma sun tsaida kudurin fice daga kasar Sin, a don haka kasar Sin tana fatan za ta daddale yarjejeniyar cinikayya da Amurka cikin sauri.

Game da wannan batu, Geng Shuang ya bayyana cewa, duk da cewa tattalin azikin duniya bai samu ci gaba yadda ya kamata ba, kuma kasashen duniya sun sha fama da matsalar rashin daidaito, da rashin tabbaci, amma tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da samun bunkasuwa a cikin watanni shida na farkon shekarar da muke ciki, har ma ya karu da kaso 6.3 cikin dari. Ana iya cewa, kasar Sin ta yi kokari, haka kuma ta samu sakamako mai armashi, wanda ya kai sahun gaba a fadin duniya.

Kakakin ya kara da cewa, daddale yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka, ba bukatar bangare guda kawai ba ne, kuma masu hangen nesa, da masu sayayya na Amurka, su ma sun nuna adawa da manufar kara buga haraji kan kayayyakin kasar Sin, haka kuma sun yi adawa da yakin cinikayyar da Amurka ta tayar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China