Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Zambia ta lashi takobin ci gaba da samar da kariya ga 'yan gudun hijira
2019-06-21 11:17:33        cri

Kasar Zambia ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen bikin ranar tunawa da 'yan gudun hijira, inda gwamnatin ta yi alkawarin ba da kariya ga 'yan gudun hijira.

Bikin mai taken 'tattaki da 'yan gudun hijira', ya gudana ne a Lusaka, babban birnin kasar, inda ya kunshi shirye-shirye daban daban na nishadi da 'yan gudun hijira suka gabatar.

Ministan harkokin cikin gidan kasar Stephen Kampyongo, ya kara jaddada kudurin gwamnatin na ci gaba da aiwatar da manufar bude kofa domin karbar mutanen dake bukatar taimako.

Ministan ya ce ranar na mayar da hankali ga kokarin da gwamnatin ke yi domin tabbatar da an taimakawa 'yan gudun hijira dake kasar wajen rayuwa cikin mutunci, bayan an tilasta musu tserewa daga matsugunansu.

Haka zalika, ya ce lokacin ne na waiwaye kan tushen abubuwan dake sabbaba daidaitar mutane da kuma abubuwan da za a yi na kare mutane daga tsallake iyakoki bisa tilas, don neman mafaka. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China