2019-07-19 10:38:59 cri |
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gana da wasu Sinawa kwanan baya a fadarsa, wadanda suka ce wai, an ci zarafinsu saboda addini a kasar Sin. Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Lu Kang ya jaddada a gun taron manema labarai da aka shirya jiya Alhamis cewa, babu wani batu mai kama da cin zarafi na addini a kasar Sin ko kadan, kuma ya kamata Amurka ta daina fakewa da batun addini tana tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe.
Lu Kang ya bayyana cewa, bahasin da wadannan Sinawa suka bayar babu gaskiya a cikinsu ko kadan, ya jaddada cewa, Sinawa na da 'yancin bin addini bisa doka. Amurka ta gayyaci mabiya haramtaccen addini na "Falun Gong" da wasu mutane dake shafawa manufar bin addini ta kasar Sin kashin kaji da su halarci taron addini, tare da ganawa da shugabannin kasar, ko shakka babu wannan mataki ya tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Bangaren kasar Sin ya bayyana matukar rashin jin dadinsa da ma adawa da wannan mataki. Don haka, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta fahimci manufofin addini da kuma hakikanin halin da Sin take ciki ta fuskar bin addini cikin 'yanci. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China