Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kura-kuranta kan binciken da aka gudanar game da saba dokar yiwa kayayyaki rangwame
2019-07-17 15:08:08        cri
Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ta bukaci kasar Amurka da ta gyara kura-kuranta na kin martaba dokar yiwa kayayyakin kasar Sin rangwame, bayan da kungiyar cinikayya ta duniya (WTO) ta ba da rahoton cewa, matakan kasar Amurka suna hannu riga da dokokin kungiyar.

Yayin da take bayyana sakamakon rahoton wani kwamitin bincike da kungiyar cinikayya ta duniya ta kafa a watan Maris na shekarar 2018, kungiyar ta yanke hukunci jiya Talata a binrin Geneva cewa, Amurka ba ta martaba tanade-tanaden dake kunshe cikin dokokin kungiyar ba, kuma sun sabawa matakan yarjejeniya cikin 11 daga cikin binciken saba ka'ida da ta gudanar kan Amurkar.

Ma'aikatar ta bayyaya cikin wata sanarwa a shafinta na Intanet cewa, rahoton ya sake tabbatar da cewa, Amurka ta sha karya matakan daidaita harkokin cinikayya kan dokokin WTO, lamarin da ya haifar da rashin adalci, da saba daidaito yanayin cinikayya na kasa da kasa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China