Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AIIB ya samu manyan nasarori cikin shekaru uku da suka gabata, in ji shugaban Bankin
2019-07-15 14:02:29        cri

Shugaban bankin samar da kayayyakin more rayuwa na yankin Asiya (AIIB) Jin Liqun ya bayyana cewa, bankin ya cimma manyan nasarori tun lokacin da ya fara aiki shekaru uku da suka gabata.

Jin Liqun ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua yayin wata zantawa a 'yan kwanakin nan cewa, bankin ya kafa ginshikin tsarin tafiyar da shi, ya kuma yi nasarar fadada yadda yake ba da rance tare da samun matsayin dan kallon MDD na din-din-din.

Jami'in bankin ya yi wadannan kalamai ne a yayin taron shekara-shekara na hukumar gudanarwar bankin karo na hudu da a kammala a birnin Luxemberg ranar Asabar din da ta gabata. A yayin taron, bankin ya kara yawan mambobinsa zuwa 100, inda aka amince da sabbin mambobi kasashen Benin, da Djibouti da Rwanda daga nahiyar Afirka.

Bankin da kasar Sin ta gabatar, ya fara aiki ne a watan Janairun shekarar 2016 da mambobi 57, inda ya mayar da hankali wajen samar da ci gaba mai dorewa ta hanyar samar da ababan more rayuwa da sauran bangarori na raya kasa a yankin Asiya da ma sauran yankuna na duniya. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China