Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin mulkin sojin Sudan ya amince da kudurin shiga tsakanin AU da Habasha
2019-07-01 11:11:33        cri

Kwamitin mulkin soji na Sudan, ya sanar da amincewa da kudurin shiga tsakani da Tarayyar Afrika (AU) da kasar Habasha suka gabatar domin warware rikicin siyasar kasar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, kakakin kwamitin Shams-Edin Kabashi, ya ce kudurin da Tarayyar Afrika ta gabatar, na kunshe da tubalin yarjejeniyar mai kyau, kuma a shirye suke su fara tattaunawar tun daga jiya.

Ya bayyana fatan samun cikakkiyar mafita da za ta karbu ga kowa nan ba da dadewa ba, karkashin inuwar AU. Ya kuma kara da cewa, ya kamata duk wani yunkurin warware matsalar ya kasance karkashin AU.

Shams-Edin Kabashi, ya kuma bayyana godiyar kwamitin ga wakilan AU da na Habasha, bisa kokarinsu na lalubo mafita ga rikicin siyasar kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China