Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar sojoji mai mulkin Sudan ta ce a shirye take ta shiga sulhu da dukkan bangarori
2019-06-23 15:57:48        cri

Mataimakin shugaban majalisar sojoji dake mulkin kasar Sudan (TMC), Mohamed Hamdan Daqlu, ya sanar a ranar Asabar cewa, majalisar ba ta da wani burin rike madafun iko kuma a shirye take ta shiga tattaunawa da dukkan bangarorin siyasar kasar.

Daqlu, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga taron dandazon jama'a a yankin gabashin Nilu zuwa gabashin babban birnin kasar Khartoum.

"Ba mu yi watsi da tattaunawar sulhu ba, amma ba za mu amince wata jam'iyyar guda daya tilo ta samu kashi 67 bisa 100 na wakilcin majalisar dokokin kasar ba," in ji Daqlu, ya buga misali da jam'iyyar adawa ta Freedom and Change Alliance.

Ya nanata cewa, majalisar sojojin kasar a shirye take ta kafa gwamnatin rikon kwarya bisa amincewar gamayyar jam'iyyun siyasar kasar.

A cewarsa, babban abin da zai iya warware rikicin siyasar da kasar Sudan ke fuskanta a halin yanzu shi ne a gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe a kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China