![]() |
|
2019-07-13 16:47:19 cri |
Wannan shi ne karo na biyu da hukumar kare hakkin dan adam ta MDD ke amincewa da kudurorin da kasar Sin ta gabatar mata wadanda suka shafi batun raya cigaba.
Kudurin ya jaddada muhimmancin gudumowar da cigaba ke bayarwa wajen cin moriyar hakkin dan adam daga dukkan fannoni, kana kudurin ya yi la'akari da cigaba da kuma tabbatar da kare hakkin dan adam da 'yancin dan adam, a matsayin wasu muhimman ginshikai wadanda ke hade da juna kuma suke taimakekeniya ga juna.
Kudurin ya bukaci dukkan kasashen duniya su raya shirin samar da dauwamamman cigaba domin tabbatar da cin moriyar hakkin dan adam, don shiryawa ga mutane kuma don mutane su ci moriya. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China