Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Uganda ta shirya tunkarar taron kolin kasa da kasa game da yawan al'umma
2019-07-12 10:46:53        cri
Kasar Uganda ta sha alwashin cigaba da kyautata shirinta na shekaru 25 game da kula da yawan al'umma, gabanin bikin ranar tunawa da yawan al'umma ta kasa da kasa a ranar Alhamis, da kuma taron kolin kasa da kasa kan yawan al'umma da bunkasa cigaba wato (ICPD), wanda aka shirya gudanarwa a wannan shekarar a birnin Nairobin kasar Kenya.

Shugabannin kasashen duniya, da masu tsara manufofin cigaba, da kwararru, za su halarci taron kolin a Nairobi, daga ranar 12-14 ga watan Nuwambar wannan shekara domin sake bibiyar ayyukan da aka gudanar a taron kolin ICPD da ya gabata wanda aka gudanar a birnin Alkahira na kasar Masar a shekarar 1994.

A wancan lokacin, shugabanni sun amince a kafa wani shiri wanda zai kunshi yadda za'a tsara hanyoyin bunkasa cigaba cikin sauri, da kyautata rayuwar al'ummomi marasa galihu, da kuma samar da dabarun zuba jari don kyautata rayuwar matasa.

Alain Sibenaler, wakilin hukumar kula da yawan jama'a ta MDD (UNFPA) dake Uganda, ya bayyanawa mahalarta taron a gundumar Adjumani dake arewacin Uganda a lokacin bikin tunawa da ranar yawan al'umma ta duniya cewa, kasar Uganda ta samu gagarumin cigaba bisa kokarin da ta yi karkashin shirin na ICPD daga shekarar 1994 zuwa yanzu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China