Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba za ta nuna bambanci ga kamfanonin waje ba in ji ma'aikatar cinikayyar kasar
2019-07-12 09:45:27        cri
Kakakin ma'aikatar cinikayyar kasar Sin Gao Feng, ya ce kasarsa, ba ta da niyyar dakushe kamfanonin kasashen ketare, za kuma ta yi tsayin daka wajen kare hakkokin su na halal.

Mr. Gao Feng ya yi wannan tsokaci ne, yayin da yake martani game da kallon da ake yiwa yanayin muhallin zuba jari na kasar Sin, yana mai cewa, ya samu wasu rahotanni dake nuna yadda wasu kamfanoni ke nuna sanyin jiki, game da yiwuwar dorewar muhallin zuba jari, sakamakon takaddamar cinikayya da kasar Amurka ta tayar.

Jami'in ya ce gwamnatin Sin na dora muhimmancin gaske, ga amfani da jarin waje, wajen samar da ci gaba. Ya ce a baya bayan nan, kasar ta fitar da karin matakai na karfafar kamfanoni masu jarin waje dake hada hada a cikin kasar. Matakan da suka kunshi aiwatar da dokokin zuba jarin waje, da kuma rage sassan da aka hana kamfanonin waje su zubawa jari a ciki.

Kaza lika ma'aikatar ta gudanar da tarukan karawa juna sani a matakai daban daban, domin jin shawarwari daga kamfanonin waje, tare da amincewa da managartan shawarwari, wadanda za su ba da damar shawo kan kalubalen da irin wadannan kamfanoni ke fuskanta.

Hakan a cewar sa, ya nuna kwazon mahukuntan Sin, na goyon bayan ci gaban kamfanonin waje dake zuba jari a cikin kasar. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China