Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da daukar matakan dakile sauyin yanayi in ji Li Keqiang
2019-07-12 09:33:22        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce Sin za ta ci gaba da aiwatar da matakan dakile mummunan tasirin sauyin yanayi, tana kuma shirin kaddamar da karin matakan karfafa tsimin makamashi, da rage hayaki mai gurbata muhalli.

Li, wanda kuma mamba ne a kwamitin koli na hukumar siyasa a kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban tawaga mai lura da sauyin yanayi, da tsimin makamashi, da rage hayaki mai gurbata iska, ya ce kasar sa, ta samu manyan nasarori a fannin kare muhallin halittu, da sauran sassan muhalli baki daya.

Firaministan ya kara da cewa, yawan sinadarin carbon dioxide a kasar Sin dake bin iska ya ragu cikin shekarun baya bayan nan, yayin da aka kara adadin ababen hawa dake amfani da nau'oin makamashi mai tsafta.

Daga nan sai ya yi kira da a kara kwazo, wajen cimma nasarar alkawarin da Sin ta yi, na kure fitar da iskar carbon dioxide, da rage dangogin carbon dake shiga iska nan da shekarar 2030 mai zuwa. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China