Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta AU za ta yi taro a Morocco
2019-06-23 15:26:42        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Morocco ta sanar cewa, majalisar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar tarayyar Afrika (AU), za ta gudanar da taro a garin Skhirat dake bakin tekun kasar Morocco a gobe Litinin.

Taron na kwanaki uku, zai gudana ne gabanin taron majalisar dake tafe wanda kasar Morocco ce za ta jagoranta, taron dai zai yi nazarin hanyoyi da matakan bunkasa zaman lafiyar Afrika, tare da duba yadda ayyukan majalisar ke gudana, har ma da nazari kan manyan kalubalolin dake tattare da shirin wanzar da zaman lafiyar Afrika, in ji sanarwar ma'aikatar harkokin wajen.

Taron zai samu halartar mambobin kasashe 15 da suka hada da Algeria, Angola, Burundi, Djibouti, Gabon, Equatorial Guinea, Kenya, Lesotho, Liberia, Najeriya, Rwanda, Saliyo, Togo, Zimbabwe da Morocco.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China