2019-07-08 14:15:13 cri |
A cikin jawabinsa, Wang Qishan ya bayyana cewa, Sin ta sa kaimi ga kafa sabuwar dangantakar dake tsakanin kasa da kasa da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, da tabbatar da ra'ayin bangarori daban daban, da fadada hanyoyin samun bunkasuwa tare, da yin mu'amalar al'adu da juna, don tinkarar sabon kalubale dake gaban dan Adam tare. Kana Sin ta yi kira ga kasa da kasa su kiyaye tunanin samun bunkasuwa cikin lumana, da sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya, da kuma kafa dokokin kasa da kasa mai adalci da dacewa tare. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China