Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoto: Matasa masu sayayya na kasar Sin na kara mayar da hankali ga kayan kawa masu tambarin manyan kamfanoni
2019-05-29 13:46:19        cri
Wani rahoto da kamfanin McKinsey&Co ya fitar ya nuna cewa, matasa masu sayayya a kasar Sin, suna kara kashe kudade wajen sayen kayan kawa masu tambari na manyan kamfanoni.

Jaridar China Daily ta yau Laraba ce ta rawaito kamfanin na McKinsey&Co na cewa, nan da shekarar 2026, yawan kudin da Sinawa za su kashe wajen sayen kayan kawa zai ninka zuwa yuan Tiriliyan 1.2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 173.6, adadin da zai kai kaso biyu bisa uku na karin yawan sayayyar kayan kawa na duniya baki daya. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China