Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta fara aikin zamanantar da muhimmin dandalin taron Afrika
2019-05-12 15:47:08        cri

Ofishin kula da tattalin arzikin Afrika na MDD (ECA) ya sanar cewa, an kulla yarjejeniya da manyan kamfanoni 3 domin gudanar da aikin gyaran muhimmin dandalin taro na Africa Hall dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha a kan tsabar kudi dala miliyan 28.2.

"Sanya hannun da 'yan kwangilar suka yi na aikin gyara babban dandalin taron na Africa Hall, ya bayyana irin girman darajar da aikin ke da shi." in ji hukumar ta ECA.

"Aikin kwangilar gyaran dandalin taron na Afrika shine mafi girma da ECA ta sanya hannu kansa tsakaninta da masu gudanar da aikin."

Aikin gyaran asalin ginin na Africa Hall ya kunshi wasu ayyuka daban daban wadanda suka hada da daidaita filin taron, da samar da sabbin hanyoyin da baki za su shiga ainihin ginin, da daga matsayin harabar ginin katangar dandalin, da samar da sabon wajen ajiye motocin baki da kuma gina hanyoyin mota a cikin harabar hukumar, in ji sanarwar.

A matsayin wani bangare na kiyayewa da farfado da kimar dadadden tarihin da dandalin ke da shi, aikin zai kunshi kafa cibiyar din din din don nuna irin dadadden tarihin da filin taron ke da shi, musamman ta yadda zai kasance wani muhimmin waje da zai dauki hankalin masu yawon bude ido a Addis Ababa, kuma zai kara jaddada muhimmancin da MDD ke nunawa ga tarihin ci gaban Afrika, in ji hukumar ta ECA.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China