![]() |
|
2019-05-20 14:14:42 cri |
Mataimakin shugaban babban bankin al'ummar kasar Sin Pan Gongsheng, shi ne ya bayyana hakan yayin wata zantawa da mujallar harkokin kudi da bankin ke wallafa.
Pan ya ce, a halin yanzu tattalin arzikin kasar na gudana bisa turba mai kyau, kamar yadda muhimman alkaluma ke tafiya yadda ya kamata, duk da koma bayana a bangaren matakan farfado ga cigaba, yayin da a hannu guda kananan sana'o'i suke ci gaba da bunkasa.
A cewarsa, tun farkon wannan shekara, kasuwar hada-hadar kudin kasar suna gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba, inda jarin waje ke kara shigowa cikin kasar, da karuwar kudaden ajiya, yayin da ake hasashen samun ingantuwar kasuwa.
Jami'in ya ce, Kasar Sin za ta kara bude kofar harkokin kudadenta ga ketare kamar yadda aka tsara, za kuma ta ci gaba da tsara managartan manufofin na bude kofa da zurfafa gyare-gyare a harkokin musayar kudaden ketarenta.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China