Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci a kawo karshen tashin hankalin Sudan
2019-06-12 10:57:04        cri

A jiya Talata MDD ta yi kiran a kawo karshen rikicin kasar Sudan, kana a dawo kan teburin tattaunawar sulhu tsakanin masu zanga zanga da majalisar sojoji mai mulkin rikon kwarya a kasar.

"Hakika muna ci gaba da bibiyar abubuwan dake faruwa game da yanayin da ake ciki a Khartoum, muna bukatar a gaggauta kawo karshen yin amfani da karfin da ya wuce kima, ya kamata a dawo kan teburin tattaunawar sulhu kan rikicin siyasar kasar." in ji Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres.

"Kuma muna bukatar hukumomin kasar da su daina kamawa tare da tsare mutanen dake taka rawar gani a tattaunawar zaman lafiya, sannan ya kamata a dawo da hanyoyin sadarwa na intanet da sauran bangarorin sadarwar kasar." Stephane Dujarric ya bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai.

Dujarric, ya kuma bukaci dukkannin bangarorin da abin ya shafa da su yi aiki tare domin tabbatar da jagorantar mika mulki ga farar hula da kuma dorewa zaman lafiya a fadin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China