Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya yi kira da a magance tushen sanadin rashin matsuguni a Afrika
2019-05-22 10:48:31        cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya yi kira da a yi kokarin magance tushen matsalolin dake raba mutane da matsugunansu a Afrika

Antonio Guterres ya shaidawa taron tattaunawa kan nahiyar Afrika da ya gudana jiya a hedkwatar MDD dake birnin New York cewa, hanya mafi dacewa ta kare masu neman mafaka da 'yan gudun hijira ita ce, kare su daga barin gidajensu, abun dake nufin magance tushen matsalolin da suka hada da talauci da fatara da dukkan nau'ikan wariya.

Sakatare janar din ya bukaci a bi ajandar muradun ci gaba masu dorewa na MDD da ake son cimmawa zuwa shekarar 2030, da ajandar tarayyar Afrika da ake son cimma zuwa shekarar 2063 a matsayin hanyoyin magance matsalolin. Ya ce dukkan muradun suna mayar da hankali ne ga jama'a da samar da sauyi a duniya, yana mai cewa, yaki da talauci shi ne muhimmin batu.

Taken da tarayyar Afrika ta zaba a bana da kuma taken tattaunawa kan nahiyar na MDD a bana shi ne, "masu neman mafaka da masu dawowa gida da wadanda suka rasa matsugunansu a kasarsu: samar da mafita mai dorewa ga abubuwan dake tilasta raba mutane da matsugunansu a Afrika".

Har ila yau, sakatare janar na MDD ya ce, kasashen Afrika sun dade suna bude iyakokin da kofofi da zukatansu ga 'yan gudun hijira da masu neman mafaka, misalin da ba ko wane a duniya ke koyi da shi ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China