Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: ana sa ran kara samun albishir daga zirin Koriya
2019-07-02 20:25:01        cri

Yau Talata ministan harkokin wajen kasar Sin Wang yi, ya ce kwanan baya, sassa daban daban masu ruwa da tsaki sun yi musayar ra'ayi yadda ya kamata kan batun zirin Koriya. Ana kuma sa ran kara samun albishir daga zirin.

Wang Yi ya fadi haka ne, yayin da ya amsa tambayar manema labaru a wajen taron manema labaru da ya yi cikin hadin gwiwa da takwaransa na kasar Mexico a nan birnin Beijing.

A ranar 30 ga watan Yuni ne, shugabannin kasashen Amurka da Koriya ta Arewa, suka gana da juna a karo na 3 a kauyen Panmunjom, inda suka cimma daidaito kan maido da tattaunawa tsakanin kasashen 2.

Dangane da lamarin, Wang Yi ya ce, ganawarsu, muhimmin mataki ne a kan turba da ta dace, wadda kasar Sin ta yi maraba da kuma nuna goyon baya. Ana kuma sa ran kara samun albishir daga zirin na Koriya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China