Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan wajen Sin: Sin za ta ci gaba da hada kai da Afirka
2019-06-24 20:39:17        cri

Yau Litinin a nan birnin Beijing, mamba a majalisar gudanrwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na Burundi Nibigira Ezechiel, da na Benin Agbenonci A. Aurelien, da na Sudan ta Kudu Nhial Deng Nhial, da kuma na Gambiya Mamadou Tangara, inda ya yi nuni da cewa, duk da cewa, yanayin da kasashen duniya ke ciki yanzu yana da sarkakiya, kuma yana yin manyan sauye-sauye, amma kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin kai dake tsakaninta da daukacin kasashen Afirka baki daya.

Wang Yi ya kara da cewa, kasar Sin tana son taimakawa ci gaban kasashen Afirka, ta hanyar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, da kuma shirye-shirye guda takwas da aka cimma matsaya a kan su, yayin taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, haka kuma tana son kara karfafa cudanyar dake tsakaninta da kasashen Afirka a fannin gudanar da harkokin kasa, kana za ta sa kaimi kan kamfanoninta, domin su kara taka rawa a harkar gina kasashen.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China