![]() |
|
2019-05-07 11:16:30 cri |
Tattalin arzikin harkokin intanet na kasar Sin, ya kai yuan triliyan 31.3, kwatankwacin dala triliyan 4.6 a shekarar 2018, wanda ya dauki kaso 34.8 na jimilar alkaluman GDP na kasar.
Rahoton da aka bayyana yayin taron na 2 na harkokin intanet na kasar Sin dake gudana a birnin Fuzhou dake yankin kudu maso gabashin kasar Sin, ya nuna cewa, tsarin kirkire-kirkire na kasar ya ci gaba da samun tagomashi. Ya kara da cewa, tattalin arzikin bangaren intanet ya inganta tare da karfafa sabbin abubuwan dake ingiza ci gaba, inda a bara, yawan cinikayya ta intanet da aka yi ya kai yuan triliyan 31.63, kana darajar kayayyakin da aka sayar ta kai sama da yuan triliyan 9. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China