Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
ILO: Karuwar zafi zai haifar da hasarar guraben aikin yi miliyan 80
2019-07-02 11:00:36        cri

Hukumar kula da ayyukan kwadago ta kasa da kasa (ILO) ta fitar da wani sabon rahoto a ranar Litinin da ya gabata, inda aka yi hasashen cewa, matsalar karuwar yanayin zafi wanda ake fuskanta a sanadiyyar dumamar duniya zai iya haddasa hasarar guraben ayyukan yi kimanin miliyan 80 nan da shekarar 2030.

Hukumar ta ILO ta nuna cewa, hasashen da aka yi game da karuwar dumamar yanayin duniya inda za'a samu karuwar zafi da maki 1.5°C zuwa karshen wannan karnin, lamarin da ake hasashe nan da 2030, kusan kashi 2.2% na lokutan aiki za'a rasa su a duk fadin duniya saboda tsananin zafi.

Kungiyar ta kiyasta guraben aikin da za'a rasa kwatankwacin miliyan 80 ya yi daidai da hasarar tattalin arzikin da ya kai na dala biliyan 2,400.

Catherine Saget, wacce ta jagoranci sashen bincike na kungiyar ILO, kana babbar marubuciyar rahoton, ta bayyana a taron manema labarai na MDD cewa, "Tasirin da matsanancin zafin zai haifarwa yanayin ayyukan kwadago ya kasance wani mummunan sakamako da aka samu daga sauyin yanayin duniya, wanda hakan zai iya shafar wasu bangarori kamar yanayin ruwan sama, da tumbatsar teku, da kuma hasarar wasu nau'ikan halittun dabbobi da tsirrai". (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China