Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An mai da hankali kan sabon kalubale a sassan ayyuka a nan gaba
2019-06-11 13:49:37        cri

Jiya Litinin ne aka bude babban taron kungiyar 'yan kwadago na kasa da kasa karo na 108 a birnin Geneva, inda aka mai da hankali kan sabbin kalubalolin da za a fuskanta a sassan ayyuka a nan gaba, wadanda yin kirkire-kirkire ta fuskar kimiyya da fasaha, sauyin yanayi da sauran batutuwa ka iya haifar.

A cikin jawabinsa a yayin bikin bude taron, babban sakataren kungiyar 'yan kwadago ta kasa da kasa wato ILO Guy Ryder ya bayyana cewa, shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 100 da kafuwar kungiyar ta ILO. Batutuwan yin kirkire-kirkire ta fuskar kimiyya da fasaha, sauyin tsarin al'umma, sauyin yanayi, dinkuwar duniya baki daya da dai sauransu suna haifar da babban sauyi kan sassan ayyuka, wanda ba a taba ganin irinsa ba tun bayan kafuwar kungiyar. Don haka, an mai da hankali kan kalubalen da za a fuskanta a sassan ayyuka a nan gaba, da damar da za a samu da zabin da za a yi.

An ce, za a kammala babban taron a ranar 21 ga wata, taron da ya samu halartar wakilai fiye da dubu 5 daga kasashe 187 mambobin kungiyar ta ILO. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China