Ranar 12 ga watan Yuni, rana ce ta yaki da sanya yara kanana ayyuka ta duniya. A cikin sanarwar da ya fitar, mista Ryder ya yi kira ga kowa da kowa a duniya da ya mai da hankali kan tasirin da rikice-rikice da bala'u suka haifarwa yara da ake sakawa aiki. Ya jaddada cewa, dole ne kasa da kasa su dauki matakai cikin gaggawa, domin daidaita wannan batu.
A wannan rana kuma, kungiyar FAO ta MDD ta ba da sanarwar cewa, baki daya an samu yara miliyan 168 dake aiki a fadin duniya, a ciki yara sama da miliyan 98 suna aikin gona. Baya rashin biyansu albashi, har ma suna fuskantar hadurra iri iri. An ba da shaida cewa, a yayin da suke aikin gona, yawan yara da matasa da suka mutu da wadanda suka ji rauni ya dara na baligai. (Fatima)