Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin ilimin tattalin arziki: Ci gaban Sin ya taimakawa tabbatar da zaman karkon tattalin arzikin duniya
2019-05-17 14:10:42        cri

Kwanan nan, hukumar kididiga ta kasar Sin ta sanar da alkaluman tattalin arzikin kasar Sin a farkon watanni 3 na bana, wadanda suka sheda cewa, yawan kudin kayayyakin da kasar ke samarwa a gida wato GDP ya karu da kashi 6.4% bisa makamancin lokacin bara. Dangane da lamarin, wani shahararren masanin ilimin tattalin arziki na kasar Amurka ya ce, yanayin da kasar Sin ke ciki ya taimakawa tabbatar da zaman karkon tattalin arzikin duniya.

Kevin Chen, shi ne masanin ilimin tattalin arziki mai matsayi na farko a kamfanin hada-hadar kudi na HFHC na kasar Amurka, wanda ya gaya ma wakilin CRI cewa, yadda kasar Sin ta kiyaye ci gaban tattalin arziki mai sauri wani abu ne mai burgewa, ya ce,

"Idan an kwatanta da sauran kasashe, za a ga karuwar da ta kai kashin 6.4% wata babbar nasara ce. Jamillar ta fi ta wasu kasashe masu sukuni, kuma ta yi daidai da alkaluman wasu kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa cikin sauri. Ta la'akari da yadda tattalin arzikin duniya ke tafiyar hawainiya a lokacin yanzu, yadda kasar Sin ta kiyaye wannan yanayi na ci gaba cikin sauri, wannan wani abu ne mai kyau soai."

A cewar Kevin Chen, karuwar GDPn ta kashi 6.4%, ta nuna yadda tattalin arzikin Sin na cikin wani yanayi mai kima. Ko da yake saurin karuwar bai kai na baya ba, amma har yanzu karuwar ta yi yawa, bisa la'akari da babban adadin tattalin arzikin da kasar ke da shi. Ban da haka, kasar Sin na karkata ga turbar neman ci gaban tattalin arziki mai inganci. Don haka, neman ci gaba cikin sauri, gami da tabbatar da ingancin ci gaban, dukkansu na da muhimmanci matuka.

Malam Chen na ganin cewa, kasancewar kasar Sin tattalin arziki mafi girma na biyu a duniya, yadda take samun ci gaba yana da ma'ana sosai ga tattalin arzikin duniya, domin ta hakan za a iya tabbatar da wani yanayi mai karko a kasuwannin kasa da kasa.

Ban da haka, alkaluman da aka samu daga hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa, yawan kudin kayayyakin da suka wuce kwastam na kasar Sin ya zarce kudin Sin RMB Yuan triliyan 7, jimillar da ta karu da kashi 3.7% bisa makamancin lokacin bara. Sa'an nan a watan Maris da ya gabata, karuwar kudin kayayyakin da aka shigar da kuma fitar da su ta kai kashi 9.6%. Yayin da karuwa a fannin fitar da kayayyaki ta kai kashi 21.3%.

Dangane da wannan ci gaba, Malam Kevin Chen ya ce, hakika kasar Sin tana kokarin habaka bukatun gida maimakon dogaro kan fitar da kayayyakinta sosai. Amma duk da haka, har yanzu kasar Sin babbar kasa ce a fannin cinikayya. Saboda haka, yadda kasar Sin ta kiyaye ci gabanta a harkar shigar da fitar da kayayyaki yana da ma'ana sosai, ga yunkurin tabbatar da karuwar ciniki a kasuwannin duniya. Malam Chen ya kara da cewa,

"Abu ne mai kyau ganin yadda kasar Sin ta kiyaye ci gaban cinikinta. Domin hakan ya shaida cewa, bukatun kasar Sin a kasuwannin sauran kasashe na ci gaba da habaka. Hakan yana da muhimmanci sosai ga tattalin arzikin duniya. Kasar Sin za ta iya taimakawa sauran kasashe samun ci gaban tattalin arziki, ta hanyar kara bude kofarta. Yadda kasar ta sanya kamfanoninta zuba karin kudade a kasashe daban daban, da yadda aka gayyaci karin kamfanonin ketare su zuba jari a kasar Sin, gami da bude kofar kasuwar hada-hadar kudi a kasar, dukkansu wasu matakai ne masu alheri da za a iya dauka."

A sa'i daya kuma, Chen ya ce, yayin da kasar Sin da kasar Amurka suke shawarwari don neman daidaita takaddamar ciniki tsakaninsu, alkaluman tattalin arziki da ciniki na kasar Sin suna ci gaba da karuwa, hakan ya sheda cewa muhalli bai yi illa sosai ga tattalin arzikin kasar Sin ba. Sa'an nan 'yan kasuwan kasar Amurka na sa ran ganin kasashen 2 su cimma daidaito. A cewarsa,

"Wadannan kasashen 2 za su zurfafa huldarsu a fannin tattalin arziki da ciniki. Yanzu ana fama da takaddama, amma ana sa ran ganin wata makoma mai haske a nan gaba."

Chen ya ce, duk da cewa yawan kudin da Sin da Amurka suke zuba wa juna ya ragu, amma 'yan kasuwan bangarorin 2 na kara nuna sanin kima yayin zuba jari, kana suna kokarin tabbatar da dorewar matakan da suka dauka. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China