Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin baje-kolin cinikayyar Sin da Afirka zai karfafa hadin-gwiwar bangarorin biyu a fannin tattalin arziki da cinikayya
2019-06-05 14:18:28        cri

Za'a yi bikin baje-kolin hada-hadar cinikayya da tattalin arziki na Sin da Afirka karo na farko, daga ranar 27 zuwa 29 ga wata a lardin Hunan na kasar Sin, inda mataimakin ministan kasuwancin Sin Qian Keming ya bayyana cewa, baje-kolin zai zama wani sabon dandali ga hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskokin tattalin arziki da cinikayya da sanya sabon kuzari ga hadin-gwiwar bangarorin biyu.

Baje-kolin hada-hadar cinikayya na Sin da Afirka karo na farko da za'a gudanar na kunshe da wasu muhimman ayyuka 14 gami da wani bikin nune-nune daya. Muhimman ayyukan 14 sun kunshi gagarumin bikin bude baje-kolin, da tarurrukan karawa juna sani hudu, da wasu shawarwari kan tattalin arziki da kasuwanci uku. Tarurrukan karawa juna sani hudun za su maida hankali kan batutuwan da suka jibanci hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fannin aikin gona da abinci, da lalibo hanyar hadin-gwiwa cikin dogon lokaci, da kara musayar dabarun inganta manyan ababen more rayuwa tsakanin Sin da Afirka. Baje-kolin a wannan karo zai kunshi wasu manyan dakunan nune-nune shida, ciki har da dakin Afirka, da dakin kananan hukumomi, da dakin kamfanoni da sauransu. Mataimakin shugaban lardin Hunan He Baoxiang ya bayyana cewa:

"Baje-kolin hada-hadar cinikayya da tattalin arziki na Sin da Afirka ya jawo hankalin mutanen ciki da wajen kasa sosai. Kawo yanzu, akwai wasu kasashen Afirka 53 wadanda suka yi rajistar halartar bikin, kana kuma wasu hukumomin kasa da kasa, ciki har da hukumar raya masana'antu ta Majalisar Dinkin Duniya, da hukumar samar da abinci ta MDD, da hukumar kula da harkokin kasuwanci ta duniya ta WTO, da kungiyar tarayyar Afirka AU, su ma za su halarci taron. Larduna gami da birane 31 na kasar Sin su ma za su halarci taron. Gaba daya akwai baki 'yan kasashen waje sama da 1500 wadanda za su zo halartar baje-kolin, kuma adadin baki daga kasar Sin zai zarce dubu biyar. Har wa yau, akwai mahalarta bikin gami da masu sayayya daga gida da waje 3500 wadanda za su halarci bikin."

Hadin-gwiwa da mu'amalar Sin da Afirka ta fuskokin tattalin arziki da kasuwanci na bunkasuwa cikin sauri. Kididdiga ta nuna cewa, jimillar kudin cinikayya tsakanin Sin da Afirka a shekara ta 2018 ta zarce dala biliyan 204, wadda ta karu da kaso 20 bisa dari. Haka kuma kasar Sin ta zama babbar aminiyar cinikayya ta farko ta kasashen Afirka a jerin shekaru goman da suka wuce, a yayin da tsarin cinikayyar bangarorin biyu ke kara samun ingantuwa. Mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin Qian Keming ya nuna cewa:

"Adadin cinikin na'urorin wutar lantarki da hajojin dake kunshe da sabbin kimiyya da fasahar zamani ya dauki kaso 56 bisa dari na dukkan kayan da kasar Sin ta fitar zuwa kasashen Afirka, kana kuma kasar Sin na kara shigowa da wasu kaya da ba na albarkatu ba daga kasashen Afirka. A shekara ta 2018, adadin kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen Afirka ya karu da kaso 32 bisa dari, kuma karuwar cinikin amfanin gona ta kai kaso 22 bisa dari. Har wa yau, kasar Sin da kasar Mauritius sun kammala shawarwarinsu kan kulla yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci, al'amarin da ya shaida cewa, an samu sabon ci gaba wajen karfafa hadin-gwiwar Sin da Afirka a tsarin cinikayya."

Ya zuwa karshen bara, yawan kamfanonin da kasar Sin ta kafa a kasashen Afirka ya zarce 3700, wadanda suka zuba jari kai-tsaye da yawansa ya wuce dala biliyan 46 a nahiyar. Domin kara zurfafa hadin-gwiwar Sin da Afirka, wasu kasashen Afirka shida, da suka hada da Masar da Angola da Kwadivwa da Senegal da Tanzaniya da kuma Uganda, za su jagoranci taron tallata kasashen Afirka ta fannin hadin-gwiwar zuba jari a wajen baje-kolin wannan karo, inda za su samu damar bayyana muhalli gami da manufofin zuba jari na kasashensu. Qian Keming ya ce:

"Dangantakar Sin da Afirka na cikin yanayi mai kyau a halin yanzu, kuma dukkansu na fatan kara yin mu'amala da cudanya ta fannin manufofin neman ci gaba. Makasudin shirya wannan baje-kolin hada-hadar cinikayya da tattalin arziki na Sin da Afirka shi ne, domin biyan sabbin bukatun da ake da su, da kafa sabon tsarin hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskokin tattalin arziki da cinikayya, wanda zai sanya sabon kuzari ga ci gaban hadin-gwiwar bangarorin biyu a sabon zamanin da muke ciki."(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China