Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta gudanar da bikin nuna fina-finai a Masar domin inganta musayar aladu
2019-07-01 10:12:14        cri

Cibiyar raya al'adu ta kasar Sin dake birnin Alkahira na Masar, ta gudanar da bikin nuna fitattun fina-finan kasar Sin ga al'ummar Masar, a wani bangare na musayar al'adu tsakanin kasashen biyu.

Bikin wanda ya samu halartar jakadan kasar Sin dake birnin, Liao Liqiang da jami'an kula da al'adu na Sin da Masar, ya gudana ne domin murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar al'ummar kasar Sin.

Yayin bikin, an nuna fitattun fina-finan kasar Sin 6, don kara fahimtar da al'ummar Masar kan al'adun kasar Sin.

Jakadan na kasar Sin, ya bayyana alaka mai karfi dake tsakanin Sin da Masar da aka kara daukaka ta zuwa muhimmin mataki, yana mai jaddada muhimmancin musayar al'adu da hulda tsakanin bangarorin biyu wajen inganta abota tsakaninsu.

Liao Liqiang, ya ce Masar ita ce kasar Larabawa ta farko, kuma kasar Afrika ta farko da ta kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin kimanin shekaru 63 da suka gabata. Kuma sauye-sauyen yanayin yanki da na duniya, ba za su sauya dangantaka mai karfi dake tsakanin kasashen biyu ba. (Fa'iza Msuatpha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China