Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hambararren shugaban Masar Morsi ya rasu a kotu
2019-06-18 11:03:58        cri

Tsohon shugaban kasar Masar Mohamed Morsi ya rasu a ranar Litinin a cikin kotu bayan kammala zaman sauraron shari'a kan zarge zargen da ake tuhumar sa da su, gidan talabijin din kasar ne ya ba da rahoton.

"Tsohon shugaban kasar ya nemi a ba shi damar yin magana inda alkalin kotun ya ba shi izini," in ji gidan talabijin na kasar. Morsi daga bisani sai ya fadi kasa kuma aka garzaya da shi zuwa asibiti. Kafafen yada labaran cikin gidan kasar sun ce tsohon shugaban kasar ya gamu da bugun zuciya ne.

Ya sha halartar zaman kotu sau da dama a birnin Alkahira bisa tuhumar da ake masa na aikata munanan laifuka tare da wasu mutane 22.

Nabil Sadek, jami'i mai gabatar da kara, ya fada cikin wata sanarwa cewa, tsohon shugaba Morsi ya yanki jiki ya fadi kasa ne a wajen da aka kebe ga mutanen dake kare kansu a kotu bayan ya yi bayani na mintoci 5 daga bisani aka ba da sanarwar mutuwarsa da misalin karfe 4:50 na yamma agogon kasar daidai da karfe (1450 GMT).

Bisa binciken da aka gudanar a kan gawarsa, babu wasu alamu dake nuna cewa akwai rauni a jikin gawar tasa, in ji Sadek.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China