Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron kolin Osaka na G20 ya nuna goyon bayan ra'ayin kasancewar sassa daban daban a duniya
2019-06-30 16:17:58        cri

An rufe taron kolin kungiyar kasashe 20, ta kasashe masu karfin tattalin arziki wato G20 a birnin Osaka na kasar Japan jiya Asabar, inda shugabannin kasashe mambobin kungiyar suka yi shawarwari daban daban da dama a tsakaninsu, lamarin da ya sanya taron kolin Osaka, zama wani muhimmin dandali na kara azama kan ra'ayin kasancewar sassa daban daban a duniya da kuma warware batutuwa masu ruwa da tsaki. Kana taron kolin, ya karfafa gwiwar kasashen duniya kwarai da gaske.

Jawaban da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi yayin taron kolin da ma wasu harkokin diplomasiyya da ya gudana tsakaninsa da bangarori daban daban, sun jawo hankalin kasashen duniya sosai. A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya sanar da wasu matakai 5 da kasar Sin za ta dauka, wadanda suka hada da kara bude kasuwarta ga kasashen ketare, da kara sayen kayayyaki daga ketare don radin kanta, da ci gaba da kyautata yanayin tafiyar da harkokin kasuwanci, da kawar da bambanci tsakanin kamfanoninta da na kasashen ketare daga dukkan fannoni, sanna za ta kara karfinta kan yin shawarwari ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, matakan da suka nuna cewa, kasar Sin ta cika alkawarinta na kara bude kofarta ga ketare, tare da ci gaba da kara kuzari kan dinkewar tattalin arzikin duniya baki daya.

Abin da ya kamata a lura da shi shi ne, shugaba Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, sun sake yin tattaunawa tsakaninsu, inda suka amince da maido da shawarwari a tsakanin kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki da cinikayya cikin adalci tare da girmama juna. Sa'an nan kuma Amurka ba za ta kara dora haraji kan kayayyakin da kasar Sin za ta sayar mata ba. Kyakkyawan sakamakon tattaunawar ya dace da ra'ayoyin jama'ar kasashen 2, ya kuma biya bukatun kasashen duniya, kana ya taimaka wajen sassauta zaman dar-dar a kasuwanni.

Haka zalika kuma, taron kolin na Osaka ya nuna cikakken goyon bayan ra'ayin kasancewar sassa daban daban a duniya, da bude kofa ga kowa, da neman samun moriyar juna da nasara tare. Don haka, Ci gaba da gudanar da harkokinta yadda ya kamata, da kuma namijin kokarin don samun ci gaba mai inganci, matakai ne da kasar Sin ba za ta canza ba, domin amfanawa jama'arta da ma duniya baki daya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China