Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kara bude kofa domin raya tattalin arzikin duniya mai inganci
2019-06-28 21:56:55        cri

A yau Jumma'a ne aka kaddamar da taron kolin shugabannin kasashen mambobin kungiyar G20 karo na 14 a birnin Osakar kasar Japan. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi yayin taron, inda ya yi kira ga sassa daban daban, da su yi kokari tare domin raya tattalin arzikin duniya mai inganci, kana ya sanar da cewa, kasarsa za ta kara daukar matakai biyar, domin kara bude kofa ga kasashen waje, ta yadda za ta taka rawa wajen kyautata tsarin kasa da kasa.

Bana ake cika shekaru goma da gamuwa da rikicin hada-hadar kudi a fadin duniya, kuma yanzu haka tattalin azikin duniya ya sake gamuwa da matsala, inda a kwanan baya, babbar jami'ar asusun ba da lamuni na duniya Christine Lagarde, ta yi nuni da cewa, kafin shekaru biyu da suka gabata, tattalin arzikin kasashen duniya kaso 75 cikin dari ya samu ci gaba cikin sauri, amma yanzu wato bana, kaso 70 cikin dari zai gamu da matsala, a don haka, ya kamata a kara mai da hankali kan batun domin tsai da kuduri mai dacewa.

Matakai biyar da shugaba Xi ya sanar sun hada da: Na farko, kasar Sin za ta sanar da jadawalin sassan zuba jarin waje da aka kayyade na shekarar 2019, inda za ta kara bude kofa ga ketare a bangarorin aikin gona, da hakar ma'adinai, da kere-kere da aikin hidima, kuma za a kara kafa sabbin yankunan cinikayya maras shinge guda shida. Na biyu, za a kara shigo da kayayyaki daga kasashen waje, tare kuma da rage buga haraji kan kayayyakin. Na uku, za a kara kyautata muhallin kasuwanci, wato za a fara aiwatar da sabuwar dokar 'yan kasuwa baki, tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2020. Na hudu, za a fara tabbatar da manufar daidaito ga 'yan kasuwa baki, ta yadda za su gudanar da harkokinsu a kasar Sin cikin lumana. Na biyar, za a ingiza shawarwarin tattalin arziki da cinikayya, domin daddale yarjejeniyar sada zumunta, domin gudanar da hadin gwiwar tattalin arziki daga duk fannoni a shiyyar, tare kuma da hanzartar tattaunawa kan zuba jari dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, da kuma tattaunawa kan cinikayya maras shinge dake tsakanin kasashen Sin da Japan da kuma Koriya ta Kudu.

A halin yanzu, ra'ayin ba da kariya ga cinikayya da ra'ayin bangare daya na ci gaba da bazuwa, kana an kawo illa ga tsarin sana'o'in duniya, da hada-hadar kudi, an kuma kara fuskantar hadari da rashin tabbaci ga tattalin arzikin duniya.

Kasar Sin ta bayar da ra'ayin bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa bisa tsarin G20, wanda ya nuna alama mai kyau ga tattalin arzikin duniya, da kawo imani ga kasuwar duniya, da kuma kawo kyakkyawar makoma ga jama'ar kasashen duniya.

A matsayin sa na mai yin kira ga sa kaimi wajen aiwatar da raya tattalin arzikin duniya mai bude kofa, shugaba Xi Jinping ya yi kira ga kasa da kasa, da su tabbatar da aikin raya tattalin arzikin duniya mai bude kofa, wanda hakan zai sa kaimi ga kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Ya ce, ya kamata a gano fasahohin Sin, da manufofin Sin a fannin bude kofa ga kasashen waje.

A halin yanzu, bunkasuwar kimiyya da fasaha ta kawo babbar dama ga kasa da kasa, wajen kyautata tsarin raya tattalin arzikinsu. Ana kuma fuskantar muhimmin lokaci na raya tattalin arzikin duniya mai inganci. Idan wasu suka bi ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, da ra'ayin bangare daya a lokacin, da tada takaddamar cinikin duniya, hakan zai haifar da hasara ga bunkasuwarsu, har ma ga dukkan duniya baki daya.

Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya yi kashedin cewa, idan kasa da kasa sun yi hadin gwiwa, da gaggauta raya tsarin cinikin duniya, da kafa tsarin ciniki mai bude kofa a fili, hakan zai haifar da kara yawan GDP na kasashe membobin kungiyar G20 da kashi 4 cikin dari. Idan kuma ba a yi hakan ba, za a tinkari koma bayan tattalin arziki a sabon zagaye.

Ana sa ran shugabannin kasashe daban daban za su yi zabi bisa hangen nesa, kuma bisa yadda tattalin arziki ke bunkasa, sa'an nan su yi hadin kai don dauka matakai tare. Kamar yadda ya kan yi, shugaba Xi ya ba da shawara a yayin taron, inda ya jaddada cewa, ya kamata kasashen kungiyar G20 su yi gyare-gyare, da kirkire-kirkire, don gano karfin samun karuwa, kuma su kyautata ayyukan gudanar da harkokin duniya bisa ci gaban zamani. Bugu da kari, su haye wahalhalu wajen warware matsalar da suke fuskanta, yayin da suke neman bunkasuwa, gami da warware sabani yadda ya kamata. Domin cimma wannan burin, ya kamata shugabannin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki, su bi yanayin dunkulewar duniya gu daya da ake ciki, kuma su rungumi juna wajen fuskantar nan gaba tare.

A ciki, wadanda suka fi muhimmanci su ne sada zumunta, da kara amincewar juna, da hadin kansu, da sassauta halin tsananin da ake ciki, da kau da cikas a gaban batun bunkasuwa, da ma neman cimma daidaito daga sabani, a kokarin sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya mai dorewa.

More kyawawan damammaki, al'adar gargajiya ce ta kasar Sin, bude kofa don bunkasawa, tare da moriyar juna buri ne na bai daya ga Sin da duniya. Ko da yaushe Sin na daukar matakan a zo a gani, wajen more fasahohin ci gabanta, da ma damammakin bunkasuwa. Bangarori daban daban, na sa ran taron kolin na Osaka, zai iya bayyana wa duniya ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da kiyaye tsarin duniya, da ma tsarin ciniki cikin 'yanci, domin bude wani sabon babi ga ci gaban tattalin arzikin duniya mai inganci. (Jamila, Zainab, Kande)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China