Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na adawa da ra'ayin ba da kariya ga harkokin kasuwanci
2019-06-27 19:17:13        cri

 

A shekarar da ta gabata, kafafen watsa labaran duniya sun rika ba da rahotannin da suka shafi tattalin arziki kamar haka, kamfanin Apple na Amurka ya rage hasashen da ya yi ga sakamakon ayyukansa, asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya rage hasashen da ya yi ga habakar tattalin arzikin duniya, tarayyar Turai wato EU,ita ma ta rage hasashen saurin bunkasuwar tattalin arziki, babban bankin kasar Japan a nasa bangare ma ya rage hasashen da ya yi ga saurin karuwar GDPn kasar da makamantansu.

Tattalin arzikin duniya wanda ke farfadowa sannu a hankali na fuskantar sabon hadari, wato ra'ayin ba da kariya ga harkokin kasuwanci wanda ke haifar da mummunar illa ga ci gaban tattalin arzikin duniya. Kasashen duniya na fatan taron kolin kasashen G20 wanda za'a bude gobe Jumma'a a birnin Osakan kasar Japan zai dauki wasu kwararan matakan tinkarar wannan ra'ayin, don maido da ci gaban tattalin arzikin duniya kan turba madaidaiciya.

A shekarar 2013, shugaban kasar Sin ya gabatar da manufar "bullo da tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa", wanda ya dace da yanayin da ake ciki, kuma biyan bukatun jama'ar kasashe daban daban, wanda kuma ya samar da shirin da ya dace wajen tinkarar kalubalen da ake fuskanta a yanzu, da za a fuskanta a nan gaba.

 

A watan Maris na bana, majalisar zartarwar kasar Sin ta zartas da dokar zuba jarin 'yan kasuwar waje, hakan ya bude wani sabon shafi na kara bude kofa ga kasashen ketare.

A sakamakon haka, kamfanonin kasashen ketare sun soma kara zuba jari a kasar Sin. Sabuwar kididdigar da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar na nuna cewa, kasar Sin ta yi amfani da jarin waje na RMB biliyan 369.06 a watanni 5 na farkon bana, wato ya karu da kashi 6.8 cikin dari. A yanayin tafiyar hawainiya da ake ciki a fannin zuba jari kai tsaye daga kasashen ketare, kididdigar ta nuna niyyar kamfanonin kasashen waje kan kasuwar kasar Sin, ta kuma nuna cewa, an jefa kuri'un amincewa kan manufar kara bude kofa ga kasashen ketare ta kasar Sin.

Yadda kasar Sin ta kara bude kofarta ba kawai ya samu jinjina daga kamfanonin kasa da kasa ba, har ma ya amfanawa sassan da ke fama da rashin ci gaba. Darektar zartaswa ta shirin kara bunkasuwa na kasar Kenya, Hannah Wanjie Ryder, ta bayyana cewa, a shekarar 2000, yawan kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen da ba na Afirka ba ya ninka kayayyakin da ta shigo da su daga kasashen Afirka har sau 44, amma yanzu, adadin ya ragu zuwa 22, hakan babban ci gaba ne. A sa'i daya kuma, yawan kayayyakin da Amurka ta shigo daga kasashen da ba na Afirka ba ya ninka kayayyakin da ta shigo da su daga kasashen Afirka har sau 43, amma adadin ya karu zuwa 70 a halin yanzu. Abin da kuma ya shaida cewa, Amurka na rufe kofarta ga kasashen Afirka. Ta yi fatan kasashe masu ci gaba za su yi koyi da kasar Sin, su kawar da shingayen ciniki, don taimaka wa kasashen Afirka wajen samun ci gabansu.

 

Akwai karin maganar nahiyar Afirka dake cewa, ko da mutum shi daya yana tafiya cikin sauri, amma hadin gwiwa ya fi tafiya mai nisa. Watakila ra'ayin bangare daya da ra'ayin bin ra'ayoyin gwamnatin kasa sun maida wasu kasashe su samu ci gaba cikin sauri, amma abubuwan dake kawo illa da hana bunkasuwar sauran kasashen duniya za su kawo hadari ga kasa kanta. Masanin tarihi na jami'ar Cambridge ta kasar Birtaniya Martin Jacques yana ganin cewa, watakila ra'ayin ba da kariya ga cinikayya da ra'ayin maida kasar Amurka a gaban kome sun samu karbuwa a halin yanzu, amma wannan ya shaida cewa, kasar Amurka ba ta da karfi sosai kamar yadda ta ke nunawa duniya. Ba za a hana aikin raya duniya bisa tsarin bai daya ba, ya kamata kasashe membobin kungiyar G20 su tsaya tsayin daka kan matakan sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya, ciki har da ra'ayin bangarori daban daban, da tsarin hukumomin bangarori daban daban, da hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban da sauransu.

Wasu masanan kasar Japan su ma sun yi kira ga kasarsu da ta inganta hadin kai tare da kasar Sin, a kokarin ingiza yunkurin dunkulewar shiyya-shiyya gu daya. An labarta cewa, a yayin taron G20, shugaban Sin da takwarorinsa na kasashen waje da dama za su gana a tsakaninsu, lamarin da ya shaida muhimmancin da shugabannin kasa da kasa ke dora wa kan yunkurin dunkulewar shiyya-shiyya gu daya da ma hadin kansu. Gaskiya, yayin da Amurka ke daukar matakin bangaranci da ma ba da kariyar ciniki, yana da matukar muhimmanci ga kasashe daban daban su kiyaye tsarin kasancewar bangarori da dama da ma sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa ga juna.

A yayin tarurukan baya na G20, kullum kasar Sin ta kan samar da dabarunta na kiyaye tsarin kasancewar bangarori da dama da ma kyautata aikin tafiyar da harkokin duniya, bisa yadda take kara bude kofarta ga waje. Sin za ta ci gaba da yin hakan a wajen wannan taro na Osaka. Wannan nauyi ne da ke bisa wuyan kasar Sin, kuma fata ne da duniya ke yi kan kasar Sin.(Murtala, Bilkisu, Lubabatu, Zainab, Kande)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China