Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a tsaya ga ainihin burin da ake neman cimmawa a taron kolin G20
2019-06-25 19:21:33        cri

A ranar Alhamis da ke tafe ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai tashi zuwa birnin Osaka na kasar Japan, don halartar taron kolin kungiyar G20 karo na 14 da za a kaddamar. Sau 7 a jere ke nan shugaban yana halarta ko kuma shugabancin taron. A tarukan da aka gudanar a baya, shugaban kasar Sin ya gabatar da ra'ayoyin kasar Sin da kuma dabarunta wajen inganta tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya, abin da ya shaida yadda kasar ta Sin ke dora muhimmanci a kan hadin gwiwar kasashen G20.

A hakika, an fara shirya taron G20 ne a sakamakon mawuyacin halin da ake ciki. A shekarar 2008, matsalar hada-hadar kudi da ta taso daga kasar Amurka ta kuma shafi duniya baki daya. Domin hana ci gaban tabarbarewar matsalar, shugabannin kungiyar G20 sun hadu a birnin Washington a karo na farko, domin su fito da dabarun tinkarar matsalar, inda kuma kasashe masu tasowa suka ba da babbar gudummawa, kuma matakan da mambobin kungiyar suka dauka sun shawo kan matsalar yadda ya kamata, sun kuma farfado da imanin al'umma dangane da kasuwanni.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, tsarin taron kolin kungiyar G20 ya canja daga tsarin tinkarar matsaloli zuwa tsarin sarrafa tattalin arzikin duniya, wanda ya kasance daya daga cikin manyan tsare-tsaren bangarori daban daban na duniya a fannin tattalin arziki. Amma bayan bayyanar tsarin ra'ayin bangare daya, da ba da kariya ga cinikkaya, da kin amincewa da raya duniya bisa tsarin bai daya, musamman mummunar takaddamar ciniki da kasar Amurka ta tada, sun yi tasiri ga kasashe membobin kungiyar G20, don haka za a kara fuskanci kalubale a gun taron kolin Osaka na kungiyar G20 a wannan karo.

Ko kasashe membobin kungiyar G20 za su shaida hadin gwiwa da imanin tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, wanda ya jawo hankalin kasa da kasa sosai. Don hakan, ya kamata a sake jaddada burin kungiyar G20 da aka tsara tun farko a yayin taron kolin wannan karo.

Kasashe membobin kungiyar G20 na da yawan mutanen da ya kai kashi 66 cikin dari na al'ummar duniya, yawan tattalin arzikinsu ya kai kashi 85 cikin dari na duniya, kana yawan cinikin dake tsakanin kasa da kasa ya kai kashi 75 cikin dari, kana yawan jarin da aka zuba a kasashen ya kai kashi 85 cikin dari. Bisa tarihin taron kolin kungiyar G20 na tsawon shekaru fiye da 10, ya nuna cewa, idan kasashe membobin kungiyar suka hada kai da cimma daidaito da juna da bude kofa, tsarin kungiyar G20 zai iya warware matsala da dawo da tattalin arzikin duniya a kan hanyar da ta dace.

A matsayinta na memba a kungiyar kasashen G20, muhimman ra'ayoyi gami da manufofin gwamnatin kasar Sin suna taka muhimmiyar rawa wajen rage damuwar da aka nuna kan harkokin kudi da shawo kan hadurra daban-daban. A yayin taron kolin G20 da aka yi a birnin Hangzhou na kasar Sin a shekara ta 2016, Sin ta bayyana wasu muhimman dabarun farfado da tattalin arzikin duniya, ciki har da daidaita manufofin tattalin arziki daga dukkan fannoni, da yin kirkire-kirkire ga salon neman ci gaba, da samar da kuzari ga harkokin bunkasuwa, da raya tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa da habaka ci gaba mai dorewa da sauransu, wadanda suka samu babban yabo daga kasashen duniya da dama. A 'yan shekarun nan, Sin tana nuna himma da kwazo wajen aiwatar da wadannan matakai, da ba da babbar gudummawa wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikin duniya mai dorewa.

A hakika ma dai, wadannan ra'ayoyin da Sin ke dauka sun bayyana burin kasa da kasa na neman ci gaba da bunkasuwa. Sakamakon ci gaban tsarin tattalin arzikin kasuwanci da ma bunkasar fasahohi, ba za a iya hana yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya gu daya ba. Amma idan takaddamar cinikayya ta kara tsananta, to ba za a iya samun farfadowar tattalin arzikin duniya ba. A sabo da haka, Japan mai masaukin baki na taron koli na Osaka na G20 ta taba yin gargadi kan ra'ayin ba da kariyar ciniki a shekarar 2019, inda jaridar Nihon Keizai Shimbun ta kasar ta nuna cewa, abu mai muhimmanci na gaggawa dake gaban G20 shi ne a kawo karshen yakin cinikayya, da fatan taron kolin zai iya raunana karfin ra'ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya.

Duk duniya na sa ran kungiyar G20 za ta iya daukar matakai na a zo a gani a maimakon yin tattaunawa kawai. Don haka ya kamata bangarori daban daban su daidaita matsayinsu, warware sabani a tsakaninsu, cimma ra'ayi bai daya, da ma inganta hadin kansu, a kokarin bude wani sabon babi yayin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar tafiyar hawainiya. (Lubabatu, Zainab, Murtala, Kande)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China