Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manyan jami'an kasashen Afirka sun nuna yabo ga kasar Sin kan yadda take kokarin cika alkawarinta na tallafawa Afirka
2019-06-30 16:30:34        cri

A jiya Asabar aka kawo karshen taron bajekolin tattalin arziki da ciniki na Sin da Afirka karo na farko, wanda ya gudana a lardin Hunan na kasar Sin. Inda manyan jami'an kasashen Afirka da suka halarci taron, suka bayyana gagarumin biki a matsayin shaida ga yadda kasar Sin take kokarin cika alkawuran da ta yi na tallafawa kasashen Afirka.

Wannan bikin da ya gudana a birnin Chang'sha na lardin Hunan ya samu halartar manyan kusoshi daga kasashe 53 dake nahiyar Afirka, inda suka yi musayar ra'ayi da abokan hulda na kasar Sin kan yadda za su karfafa hadin gwiwa a fannin ciniki, da aikin raya kayayyakin more rayuwa, da hada-hadar kudi, da dai sauransu. Cikinsu mista Edward Boateng, jakadan kasar Ghana a kasar Sin, ya shaidawa wakilinmu cewa bikin nan na da ma'ana sosai,

"Wannan biki wani mataki ne da aka dauka don cika alkawarin da kasar Sin ta yi a wajen taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a bara. Ta hanyar gudanar da bikin, an baiwa gwamnatoci da kamfanoni na kasashen Afirka da kasar Sin damammakin habaka hadin kai, musamman ma a fannin kasuwanci. Dole ne a raya kasuwanci, sa'an nan za a samu damar rage talauci a Afirka, da kyautata zaman rayuwar jama'ar can."

A nashi bangare, gwamnan jihar Jigawa ta kasar Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce a wajen taron da ya gudana a Beijing, Najeriya da Sin sun kulla yarjeniyoyi da yawa a bangarorin shimfida layin dogo, da ma'aikatar samar da wutar lantarki, da zuba jari ga jihohi irinsu Lagos da Ogun. Sa'an nan jihar Jigawa ita ma ta samu moriya bisa hadin gwiwa da lardin Hunan na kasar Sin a fannin aikin noma. Ya ce,

"Ka san wannan lardi na Hunan, lardi ne da ya shahara a kan noman shinkafa, wanda yake muna aiki da su a Najeriya, domin habaka irin shinkafa, wanda zai ba manomi kyakkyawan sakamako. Wato su a nan kamar dukkan gaba daya wato hekta daya su kan samu ton 12 zuwa 16, wanda abin da mu kan samu a can ba ya wuce ton 2.5 zuwa ton 5. Wannan dama ne da muka samu na mu yi aiki tare, muna gwadawa, zuwa wani lokaci muna tabbatar da cewa, manomanmu za su iya noman shinkafa, kuma su sami a kalla ton 9 zuwa 10 na shinkafa a kan hekta guda 1. Bayan wannan akwai kananan injuna na aikin noma domin su rage wahalhalun noma da hannu, kuma su sa samari su shiga harkar noma."

Ban da wannan kuma, dangane da zargin da wasu kasashen yammacin duniya suke wa kasar Sin, na jefa kasashen Afirka cikin " tarko na bashi", gwamnan na jihar Jigawa ya ce wannan zargi ba shi da gaskiya. A cewarsa,

"Magana ita ce, idan an ce 'Zo ga bashi', in ka ga za a iya cin bashi nan, zai taimaki jama'ar ka, ka ci. In ka ga ba zai taimaki jama'arka ba, za ka zama bawa, ka bari. Babu abin dole a ciki. Sun zo da tsaruka na taimako da yawa, wanda yake suna yi, kuma sun zo da tsaruruka na ba da bashi ga kasashen Afirka, domin su habaka tattalin arzikinsu, wannan kuma ana yi. Ya danganta ga kasa, inda ta karbi wannan abu, ta inganta tattalin arzikinta, ita ma wata rana ta zama kamar kasar Sin. In kuma ba ta inganta ba, ta kashe kudi wajen rashin amfani, to ta zama baiwa."

Ban da wannan kuma, ministan aikin gini na kasar Ghana, Samuel Atta Akyea, ya ce yana son yin amfani da wannan dama don neman habaka hadin gwiwa da kasar Sin a fannin gina kayayyakin more rayuwa. Ya ce,

"Bikin na da muhimmanci, musamman ma kan wani bangare da kowa ya sani, wato: Idan babu kayayyakin more rayuwa masu inganci, ba za a samu damar raya tattalin arziki ba. A ganina, kasar Sin tana kan gaba a duniya wajen kokarin taimakawa kasashen Afirka raya kayayyakin more rayuwar jama'a."

Wannan biki na bajekolin tattalin arziki da ciniki na Sin da Afirka za a ci gaba da gudanar da shi bayan duk shekaru biyu, tare da nufin mai da yarjeniyoyin da aka kulla tsakanin Sin da Afirka zama hakikanan matakai, da za su amfanawa jama'ar bangarorin 2.(Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China