Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana na Sin da Afirka na tattaunawa kan inganta hadin kan bangarorin biyu don moriyar juna
2019-05-24 15:16:29        cri

A Jiya Alhamis ranar 23 ga wata ne, aka bude taron dandalin tattaunawa tsakanin masanan Sin da Afirka a Lusaka, babban birnin kasar Zambia, inda masana, jami'ai da mutanen sassa daban daban na Sin da wasu kasashen Afirka suka tattauna kan kyakkyawar damar da shawarar "ziri daya da hanya daya" da ma dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka na FOCAC ke kawowa ci gaban Afirka da Sin.

Wannan taron dandalin tattaunawa tsakanin masanan Sin da Afirka ya jawo halartar wakilan kasar Sin da na kasashen Afirka kusan 20 ciki har da Zambia, Zimbabwe, Kenya, Malawi da dai sauransu. A yayin taron da ofishin jakadancin Sin da ke Zambia da cibiyar sanya ido da nazari kan manufofi na Zambia suka kira tare, an tattauna kan yadda za a yi amfani da shawarar "ziri daya da hanya daya" da ma dandalin FOCAC wajen sa kaimi ga ci gaban kasashen Afirka, a kokarin cimma moriyar juna da samun bunkasuwa tare a tsakanin bangarorin biyu.

A jawabinsa na bude taron, Li Jie, jakadan Sin da ke Zambia, ya bayyana cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" da dandalin FOCAC sun riga sun zama muhimman tsare-tsare biyu na hadin gwiwar a zo a gani tsakanin Sin da Afirka ciki har da Zambia, wadanda suka amfana wa jama'a sosai, don haka sassan biyu za su ci gaba da inganta hadin kansu a karkashin inuwar tsare-tsaren biyu. Yana mai cewa,

"Shawarar 'ziri daya da hanya daya' da dandalin FOCAC ba tarkon bashi ba ne, fanke ne da ke kawo wa jama'a alheri. Sin na son hada kai da kasashen Afirka domin neman samun dauwamammen ci gaba mai inganci da alfanu, a kokarin cimma moriyar juna da samun bunkasuwa baki daya."

Tsohon shugaban kasar Zambia Kenneth Kaunda mai shekaru 95, wanda ya kafa kasar, shi ma ya halarci bikin. A cikin jawabin da ya yi, ya ambaci shirin shimfida layin dogo tsakanin Tanzania da Zambia wanda kasar Sin ta ba da taimako wajen gina shi a shekaru 70 na karnin da ya gabata, inda ya ce, layin dogo tsakanin Tanzania da Zambia misali ne na hadin gwiwar Sin da Afirka cikin sahihanci. Ya kara da cewa,

"A wancan lokacin, gwamnatocin sauran kasashen duniya da kungiyoyin duniya ba su so su taimaka wajen shimfida layin dogon, sai dai kasar Sin ta kebe makudan kudade da ma'aikata da yawa don taimaka mana wajen shimfida layin dogon mai tsawo kilomita 1800. Wannan layin dogo wanda ake kira da 'hanyar samun 'yanci' ya samar mana sabuwar hanyar zuwa teku."

Kenneth Kaunda ya yi kira ga kasashen Afirka daban daban da su ci gaba da inganta hadin kai da zumunci da kasar Sin. A cewarsa, Afirka na da babban karfin sirrin bunkasuwa, hadin kai da Sin kuma zai kawo mata dimbin zarafin ci gaba.

A nata bangaren kuma, Madam Margaret Mwanakatwe, ministar kudin Zambia, kuma shugabar cibiyar sanya ido da nazarin manufofin kasar ta furta cewa, a cikin shekaru da dama da suka gabata, ana raya hadin gwiwa na aminci a tsakanin Sin da Afirka yadda ya kamata, Sin ta zama abokiyar ciniki mafi girma ta Afirka a shekaru 9 a jere. A matsayinsu na kasa mai tasowa mafi girma a duniya da ma nahiyar da ta fi yawan kasashe masu tasowa, Sin da Afirka na da makoma ta bai daya. Don haka Madam Mwanakatwe ta yi kira ga kasashe daban daban na Afirka da su hada tsare-tsaren ci gabansu tare da shawarar "ziri daya da hanya daya". Ta ce,

"Ya kamata hanyoyin raya kasa da kasashen Afirka suka zaba su dace da burin samun ci gaba nan da shekarar 2063 da kungiyar AU ta gabatar. Ban da wannan kuma, ya kamata mu daidaita tsare-tsarenmu domin hada su da shawarar 'ziri daya da da hanya daya', a kokarin sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Afirka, da ma kyautata zaman rayuwar jama'armu."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China