Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da takwarorinsa na wasu kasashen Afirka
2019-06-24 12:53:16        cri

Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin, ya gana da takwarorinsa na kasashen Saliyo, Gabon, Kamaru, Sao Tome da Principe, Somalia, Madagascar, jamhuriyar Congo, da Senegal, a jiya Lahadi.

Yayin ganawarsa da Madam Nabeela Tunis, ministar harkokin waje ta kasar Saliyo, mista Wang Yi ya ce, Sin da Saliyo aminai ne, wadanda a koda yaushe suna fahimtar juna, da kokarin rufawa junansu baya. Ya ce, ya kamata a yi kokarin hada shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da kasar Sin ta gabatar, da tsare-tsaren raya kasa ta kasar Saliyo, don neman karfafa hadin gwiwar bangarorin 2 a fannonin raya kayayyakin more rayuwa, da aikin noma, da na kiwon kifaye, da aikin likitanci, da sadarwa, da dai makamantansu. Sa'an nan a nata bangare, Madam Nabeela Tunis ta ce kasarta na son zurfafa abokantaka da kasar ta Sin, da musayar ra'ayi da ita kan ayyukan cika burin da MDD ta sanya na samun ci gaba mai dorewa a shekarar 2030, da dai sauransu.

Sa'an nan yayin da mista Wang Yi ke ganawa da takwaransa na kasar Gabon, ya ce, wannan taron da aka shirya na masu kula da ayyukan tabbatar da sakamakon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a birnin Beijing a bara, ya samu halartar tawagogi na manyan jami'ai na wasu kasashe 53 dake nahiyar Afirka, cikinsu har da ministocin waje na wasu kasashe 25. Hakan, a cewar ministan wajen kasar Sin, ya nuna zumunci mai zurfi dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da yadda kasashen Afirka suke dora cikakken muhimmanci kan huldar dake tsakanin bangarorin 2. Ya ce taron ya zama wata muhimmiyar dama domin kasashen Afirka da kasar Sin su karfafa hadin kansu ta fuskar manyan tsare-tsare.

Banda wannan kuma, lokacin da ministan kasar Sin ya gana da Naina Andriantsitohaina, ministan harkokin waje na kasar Madagascar, Wang Yi ya ce, kasar Sin zata ci gaba da kokarin nunawa kasar Madagascar goyon baya, bisa burinta na tabbatar da 'yancin kan kasa, da mulkin kai, da kuma sauran bukatun kasar. A cewar mista Wang, kasar Sin na son zurfafa hadin kanta da kasar Madagascar, musamman ma a fannonin zuba jari, da makamashi, da raya kayayyakin more rayuwar jama'a, da aikin gona, da ayyukan hana bazuwar cututtuka, da dai sauransu. A nasa bangare, mista Naina Andriantsitohaina ya ce, kasar Madagascar tana dora muhimmancin gaske kan huldar dake tsakaninta da kasar ta Sin, kuma tana tsayawa kan manufar kasacewar kasar Sin daya tak a duniya. Kasar Madagascar zata yi kokarin zurfafa hadin gwiwarta da kasar Sin.

Sa'an nan, yayin da mista Wang Yi ke ganawa da Jean Claude Ngakosso, ministan harkokin wajen jamhuriyar Congo, mista Wang ya ce, kasar Sin tana rungumar ra'ayin kasancewar bangarori daban daban a duniya, kuma tana kin amincewa da matakan kashin kai, da na babakere. Ya ce kasar Sin ta dauki wannan matsayi ne don kare moriyar kanta, gami da neman tabbatar da adalci a duniya, da kare moriyar bai daya ta sauran kasashe kanana da matsakaita. A nasa bangare, mista Ngakosso ya ce, matsayi mai dacewa da kasar Sin ta dauka abin yabawa ne, kasarsa ta jamhuriyar Congo zata ci gaba da tsayawa tare da kasar Sin.

Daga bisani, yayin da mista Wang Yi ke ganawa da Amadou Ba, minista mai kula da harkokin wajen kasar Senegal ya ce, Senegal ita ce kasa ta farko daga yammacin Afirka data fara halartar shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya. Yayin da a nasa bangare, Amadou Ba ya ce, ci gaban kasar Sin ya haifar da ci gaban tattalin arzikin duniya, da tabbatar da makoma mai haske ga jama'ar nahiyar Afirka. A cewarsa, hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Afirka abin koyi ne ga sauran kasashe yayin da suke neman hadin gwiwa a tsakaninsu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China