Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump: Ganawa da shugaba Xi ta samu babban sakamako
2019-06-29 19:40:06        cri

Yau da yamma, agogon Osakar Japan, shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya bayyana bayan da ya yi ganawa da shugaba Xi Jinping na kasar Sin a birnin cewa, ganawar da suka yi ta samu babban sakamako fiye da kima, kuma yanzu haka an riga an sake farfado da huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.

Trump ya kara da cewa, sassan biyu za su ci gaba da tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya, kuma Amurka za ta soke kudurin da ta tsai da kwanakin baya game da kara sanya haraji kan kayayyakin da Sin za ta shigar kasar, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 300.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China