Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin ta bukaci Amurka da ta samar da dama ga hadin gwiwa tsakanin kamfanonin kasa da kasa
2019-06-24 20:34:21        cri

Yau Litinin kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana kan batu game da kamfanin jigilar kayayyaki cikin sauri na FedEx na kasar Amurka, wanda ya mayar da wayar salula samfurin Huawei ba bisa bukatar mai jigilar ta ba, cewa kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina aikata hakan, ta kuma gyara kuskure domin samar da damar gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin kamfanonin kasashe daban daban.

An ce, sashen edita na mujallar PC ta Amurka dake Birtaniya ya aika wata wayar salula samfurin Huawei P30 zuwa ga sashen editarta dake Amurka, domin tantancewa, amma kamfanin jigilar kayayyaki cikin sauri na FedEx na kasar Amurka, ya mayar da wayar Birtaniya bisa dalilin sabawa umurnin da gwamnatin Amurka ta bayar kan kamfanin Huawei.

Kakakin ya kara da cewa, wannan ba shi ne karo na farko da kamfanin ya aikata irin wannan kuskure ba, kuma ya kamata ya yi bayani kan batun, haka kuma ya sauke nauyi dake bisa wuyansa kan wannan kuskure.

Ya ci gaba da cewa, bai kamata ba Amurka ta matsa lamba ga kamfanin kasar Sin bisa dalilin tsaron kasa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China