Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin ya rubuta rahoto kan cinikin Sin da Amurka a jaridar China Daily
2019-06-11 10:10:57        cri

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Ma Zhaoxu ya rubuta wani rahoto game da batun tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka a jaridar China Daily a ranar 7 ga wata, inda ya yi kashedin cewa, matakin nuna fin karfi da Amurka ke dauka a bangaren cinikayya yana kawo babbar illa ga daukacin kasashen duniya.

A cikin rahoton da ya rubuta tare kuma da sakaya sunansa, jakada Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, Amurka ta tayar da yakin cinikayya kan kasar Sin, lamarin da ba lalata moriyar kasashen biyu kadai ya yi ba, har ma da lalata moriyar sauran kasashen duniya baki daya, a don haka ya dace a nace ga manufar gudanar da harkokin cinikayya dake tsakanin bangarori daban daban, ta yadda za a samu moriya tare. Ya ce ba zai yiwu a hana cudanyar tattalin arziki a fadin duniya ba. Game da matakin nuna fin karfi kuwa, ya ce dole ne a mayar da martani, saboda akwai yiwuwar ko wace kasa za ta gamu da matsalar da matakin zai kawo mata.

Jakadan ya kara da cewa, dalilin da ya sa ba a samu ci gaba ba yayin tattaunawa tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka laifin Amurka ne, domin kasar Sin tana son daidaita takaddamar ta hanyar tattaunawa bisa tushen martabar juna da moriyar juna.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China