Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Barazanar Amurka ba za ta firgita Sinawa ba
2019-06-27 19:26:09        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, burin kasar Sin a kullum shi ne daidaita takaddamar tattalin azriki da cinikayyar dake tsakaninta da Amurka ta hanyar tattauna da tuntubar juna, amma fa za ta kare 'yanci da kuma muradunta.

Mr. Geng ya bayyana haka ne yau a birnin Beijing, yayin da yake mayar da martani kan kalaman shugaba Donald Trump na Amurka, cewa Amurka za ta kara sanyawa kasar Sin haraji, idan har sassan biyu ba su cimma yarjejeniya a yayin taron kolin kungiyar G20 ba.

Jami'in na kasar Sin ya bayyana cewa, barazanar Amurka na kara sanyawa kasar Sin haraji, ba zai firgita Sinawa ba. Bugu da kari, ya shawarci bangaren Amurka cewa, yakin ciniki da buga haraji ba za su yi illa ga kowa ba da ma kasar Sin, kana ba za su magance matsalar ba ko kadan.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China