Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira da a hada hannu wajen tunkarar sauyin yanayi
2019-06-29 15:40:44        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya yi kira ga bangarori daban daban, su girmama alkawarinsu na daukar kwararan matakan tunkarar sauyin yanayi.

Wang Yi ya yi kiran ne yayin wani taro da takwaransa na Faransa Jean Yves Le Drian da sakatare janar na MDD Antonio Guterres, da ya gudana a gefen taron kungiyar G20 a birnin Osaka na Japan.

Ya kuma jadadda cewa, ya kamata su kasance da kwarin gwiwa da juriya yayin tunkarar matsalar sauyin yanayi. Ya ce da farko, ya kamata su karfafa yakinin da suke da shi da kuma fafutukar samun muhallin da ya dace da za su tunkari sauyin yanayi a duniya. Na biyu, ya kamata su kiyaye ka'idoji da tabbatar da adalci da tsarin dangantakar kasa da kasa da kuma la'akari da mabanbanta nauyin dake wuyansu da kuma karfinsu, sannan su martaba yanayi na musammam na kasashe masu tasowa. Ya ce na uku kuma, za su dauki ingantaccen matakin gaggauta raya muhalli da rage fitar da sinadarin Carbon ta hanyar hada tunkartar sauyin yanayi da kara bunkasa tattalin arziki. Kana na hudu, ya kamata su rungumi hadin gwiwa da yin aiki tare. Bugu da kari, Wang Yi, ya ce ya kamata kasashe masu karfin tattalin arziki su cika alkawarin da suka dauka na taimakawa kasashe masu tasowa kara karfinsu a wannan fannin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China