Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira taron manema labarai dangane da halartar taron kolin G20 da shugaban kasar zai yi
2019-06-24 14:45:12        cri
Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta kira taron manema labarai a yau Litinin, inda mai taimakawa ministan harkokin waje na kasar Zhang Jun, da mataimakin ministan kasuwanci na kasar, wanda kuma shi ne mataimakin wakilin shawarwarin harkokin cinikayya a tsakanin kasa da kasa Mr. Wang Shouwen, tare kuma da mataimakin shugaban babban bankin kasar Sin, Chen Yulu sun yi bayani game da halartar taron kolin kungiyar G20 da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi.

Mr.Zhang Jun ya ce, daga ranar 28 zuwa 29 ga wata, za a gudanar da taron kolin kungiyar G20 karo na 14 a birnin Osaka na kasar Japan. Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron, tare da halartar shawarwarin da za a yi dangane da tattalin arziki da cinikayya na duniya, da tattalin arziki na zamani da dauwamammen ci gaba, da manyan ayyukan more rayuwa, da yanayi da makamashi da muhalli da sauransu, inda zai bayyana ra'ayoyinsa dangane da yanayin tattalin arzikin duniya, tare da gano bakin zaren warware matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China