![]() |
|
2019-06-25 20:29:08 cri |
Mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan ya bayyana kudirin kasarsa, na raya tattalin arziki mai inganci da zai amfani duniya baki daya.
Wang ya bayyana hakan ne yau Talata, yayin ganawa da wakilan kasashen duniya dake halartar taron manyan jami'ai karo na 17 dake gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Ya ce, galibin kasashen duniya sun taba dandana wahala da ma nasara, kana wayewar kan dan-Adam ta yi tasiri a cikin musayar moriyar juna da ma gado tsakani mabambanta wayewar kai.
Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, mafarkin kasar Sin da wayewar kanta na shekaru 5,000, shi ne na samun ci gaba da dawo da nasarori na tarihi. Ci gaban kasar Sin yana tafiya da ci gaban duniya, kana matsalolin da duniya ke fuskanta, sun faru sakamakon rashin daidaiton ci gaba yayin da duniya ke kara dunkulewa waje guda.
Ya ce, za mu yi abin da ya dace, da neman magance matsaloli da rashin daidaiton ci gaba da rashin bunkasuwa da kuma raya tattalin arziki mai inganci da zai amfani duniya baki daya.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China