Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan wajen Sin: Ana gudanar da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka cikin sahihanci
2019-06-24 20:37:01        cri

Yau Litinin a nan birnin Beijing, mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na Zambiya Joseoh Malanji, da na Cape Verde Luis Filipe Tavares, da na Liberiya Gbehzohnga R M. Findley, inda ya yi nuni da cewa, kasarsa tana gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninta da kasashen Afirka, bisa sahihanci ba tare da cimma muradun siyasa ba.

Wang Yi ya kara da cewa, har kullum kasar Sin tana nacewa kan manufar rashin tsoma baki a cikin harkokin cikin gida, haka kuma tana gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninta da kasashen Afirka, bisa tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa domin samun ci gaba tare da su.

Wang Yi ya jaddada cewa, Afirka babban dandalin hadin gwiwa ne na kasa da kasa, amma ba nahiyar gogayyar dake tsakanin manyan kasashe ba ce. Kuma kasashen Afirka sun fahimci wace kasa ce ke dora muhimmanci kan su, da kuma wadda take girmama, da kuma goyon bayan su. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China