Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe 53 daga Afirka za su halarci baje kolin cinikayyar Sin da Afirka
2019-06-04 18:58:45        cri

Kasashe 53 daga nahiyar Afirka ne suka bayyana aniyar su, ta halartar baje kolin hada hadar cinikayya da tattalin arziki na Sin da Afirka karo na farko, wanda zai gudana a birnin Changsha na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin. Mashirya bikin na baje koli sun bayyana cewa, za a gudanar da shi ne tsakanin ranekun 27 zuwa 29 ga watan nan na Yuni.

Yayin wani taron manema labarai, mataimakin gwamnan lardin na Hunan He Baoxiang, ya ce kungiyoyin kasa da kasa da suka tabbatar da za su aike da wakilai wurin baje kolin, sun hada da hukumar MDD mai rajin bunkasa masana'antu, da shirin abinci na MDD, da kungiyar cinikayya ta duniya.

Ana dai sa ran taron na baje koli, zai tattaro baki daga kasashen waje sama da 1,500, da wakilai na cikin kasar ta Sin sama da 5,000, baya ga masu baje hajoji sama da 3,500. Sauran sun hada da masu sayen hajoji, da kwararru masu ziyara.

He Baoxiang ya kara da cewa, kawo yanzu an tsara gudanar da wasu ayyukan hadin gwiwa, wadanda suka kunshi kasashen Afirka 39. Kaza lika ana fatan sanya hannu kan yarjejeniyoyin da suka jibanci zuba jari da cinikayya.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China