Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar harajin Sin: Matakin Amurka na tsawaita lokacin wucin gadi ba zai canja yunkurinta ba
2019-06-06 20:49:50        cri

Yau Alhamis 6 ga wata, jami'in ofishin hukumar kula da aikin tsara harajin kwastam ta majalisar gudanarwar kasar Sin ya ce, "Mun lura cewa, ofishin wakilin tattauna cinikayya na Amurka ya sanar da cewa, zai ci gaba da kara buga harajin kwastam ga kayayyakin da suka bar kasar Sin kafin ranar 10 ga watan Mayun bana, kuma za su shiga kasar Amurka kafin ranar 15 ga watan Yunin shekarar nan, da kaso 10 bisa dari", game da hakan, jami'in ya bayyana cewa, matakin da Amurka ta dauka ba zai canja yunkurinta, na kara harajin tun daga ranar 10 ga watan Mayun bana ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China