Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar kasuwancin Sin ta fitar da rahoton nazarin moriyar Amurka a cinikinta da Sin
2019-06-06 19:37:41        cri

A yau Alhamis ne ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar da wani rahoton nazari kan moriyar da kasar Amurka ta samu, yayin da take gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin a bangaren tattalin rziki da cinikayya, inda aka bayyana cewa, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayyar dake tsakanin sassan biyu, ya kawo babbar moriya ga kasashen biyu, da al'ummominsu baki daya, haka kuma Amurka ita ma ta samu babbar moriya daga hakan. An ce gibin kudin da Amurka take fuskantar yayin da take gudanar da harkokin cinikayya da kasar Sin, ya faru ne saboda matakin kayyadewa da take dauka, yayin da take fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin. Kana an ga sakamakon ne, domin dalilai da dama a bangarori daban daban. Misali takarar sana'a, da tsarin tattalin arziki, da manufar cinikayya, da matsayin kudin dala da sauransu, don haka alal hakika Amurka ba ta yi hasara ba.

Rahoton ya yi nuni da cewa, bisa alkaluman da ma'aikatun kasuwancin kasashen Sin da Amurka suka samu, bayan da suka yi nazari cikin hadin gwiwa, an lura cewa, hasashen da aka yi kan adadin kayayyakin da Amurka ta fitar zuwa kasar Sin ya yi yawa fiye da kima, har ya kai kaso 21 bisa dari a shekarar 2015. Bisa wadannan alkaluma ana iya ganin cewa, gibin kudin Amurka a bangaren fitar da kayayyakinta zuwa ga kasar Sin, bai kai adadin yawan da ake zargi ba, inda ya tsaya kan dalar Amurka biliyan 88 a shekarar 2018. Ana iya cewa, duk da cewa, kasar Sin ta samu rarar kudi yayin da take gudanar da harkokin cinikayya da Amurka, amma sassan biyu wato Sin da Amurka suna samun moriyar juna.

Rahoton ya nuna cewa, yanzu haka hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka, ya riga ya samu babban sakamako, sakamakon da ya dace da ci gaban tarihi. A don haka ya dace a kara sa kaimi kan cudanyar tattalin arziki a fadin duniya, ta yadda za a kara samun moriya daga bangaren. Ana sa ran sassan biyu wato Sin da Amurka, za su kara himmantu kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya mai inganci dake tsakaninsu a nan gaba, domin amfanin al'ummonin kasashen biyu duka, tare kuma da taimaka wa karuwar tattalin arziki da wadatar duniya baki daya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China